
Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Izala.
Malam Ibrahim Matayassara ne ya fito ya ce yana jawo hankali ga Farfesa Sheikh Sani Rijiyar Lemu da cewa ya rika girmama malamai na zamaninsa ya daina tunanin shine ya fi owa ilimi.
Sannan Yace shi fadakarwa ce yayi ga Sheikh Rijiyar Lemu ba rashin kunya ba.
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu malamai suka fito suka yi Allah wadai da wadannan kalamai nasa