
Tauraron fina-finan Hausa, Abdullahi Dan Mama wanda aka fi sani da Horo Dan mama na ci gaba da shan tofin Allah tsine bayan da yayi kira ga shugaban Izala, Sheikh Bala Lau ya fito ya kare kansa kan zargin da ake masa.
Horo Dan mama ya wallafa Bidiyon ta sigar barkwanci yana kira ga Sheikh Bala Lau ya fito da takardu a yi bincike kan lamarin zargin da ake masa.
Saidai da yawa sun mai Allah wadai da wannan abu da yayi.