
Shugaban jam’iyyar APC, Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan Kanone kuma sunansa Ashiru.
Ya bayyana cewa da aka kaishi Legas ne sai yarbawa suka mayar dashi Asiwaju.
Yace kuma dayan sunansa shine Bala inda Yarbawa nan ma suka mayar dashi Bola.
Gandune ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sadarwa.