
Tsohonnan da Bidiyonsa ya watsu sosai yana fadin cewa shine ya gina kabarin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
A yanzu ya sake yin wata hira i da yace karya yayi, bashine ya gina kabarin tsohon shugaban kasar ba.
A baya dai an jishi yana cewa ba’a biyashi kudin ginin kabarin da yayi ba.
An dai samu wani ya aika masa da Naira dubu 10 kyauta.
Saidai rahotanni sun ce ya fito ya karyata kansa ne bayan da yayi ikirarin cewa, ba’a biyashi kudin tonon Kabarin ba.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai.