
Wani matashi dan kudu me suna Scott Iguma ya bayyana cewa, sai da ya zubar da hawaye saboda yanda ya ga aka kashe Janar Muhammad Uba.
Yace bai ji dadin yanda ya ga Bidiyon na ta yawo a kafafen sada zumunta ba inda yace yanzu yaya iyalansa zasu ji idan suka ga Bidiyon.
Sannan kuma yace ganin Bidiyon zai iya ragewa Sojoji karfin Gwiwa.