
Bayan da Kiristoci suka kai kara kasar Amurka kan asarar rayukan da aka musu, Wanda hakan yasa shugaban kasar Amurka, Donald Trump bayyana cewa zai dauki mataki akan Najeriya.
Suma wasu musulmai daga Arewacin Najeriya sun fito suna bayyana irin Asarar rayukan da rikice-rikice sukawa musulmai.
Bidiyon su ya watsu sosai inda mutane suka rika bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.