
Wata sabuwar masifa da ta shigo kafafen sada zumuntar Arewa itace ta amfani da wani AI ana saka hotunan malamai ana sawa su yi rawa.
Wannan AI a baya ‘yan siyasa kawai akewa amfani dashi amma yanzu lamarin ya kai har kan malamai.
Wasu daga cikin Malam da muka ci karo an yi Amfani da wannan AI din an sa sun yi rawa sun hada da Marigayi Shaikh Jafar Adam, da Sheikh Bala Lau da Sheikh Maqari.
Wani abin takaici ma shine lamarin ya koma gasa tsakanin matasa mabiya akidu, idan wannan ta saka malamin wannan akida rawa, sai shima wancan ya rama.
Fatan mu anan shine Allah ya kawo mana karshen wannan lamari dlya kuma shirya masu yi su gane hakan ba daidai bane.