Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, hukumomin ‘yansandan Najeriya sun kama ‘yan kasar China 80 suna laifukan damfarar yanar gizo.
A wani Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda aka kama ‘yan kasar ta China da yawa.
An kuma kwace kwamfutoci da wayoyi da dauransu.