
An Hango jirgin saman sojojin Najeriya C-130 dake ajiye a filin jiragen saman kasar Burkina Faso.
Jirgin dai na dauke da sojoji 11 ne na Najeriya da hukumomin Najeriya suka ce ya samu tangarda a hanyarsa ta zuwa kasar Portugal ya sauka a kasar ta Burkina Faso.
Saidai hukumomin kasar Burkina Faso sun zargi akwai wata maqarqashiya game da saukar jirgin a kasarsu.