
Faston nan na kasar Ghana da ya ce wai an masa Wahayi Duniya zata tashi ranar Kirsimeti watau 25 ga watan Disamba kuma wai an ce masa ya kera jiragen ruwa 8 dan ya kwashi mutane a ciki saboda za’a yi ruwa irin na Dufana a yanzu ya fito yanawa mabiyansa bankwana.
Rahotanni sun ce wadanda suka yadda dashi tuni suka sayar da kadarorinsu suka koma wajansa da zama inda suke jiran ranar 25 ga wata tazo.
An ganshi ya fito yanawa mabiyan nasa bankwana.