
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana takaici kan yanda yace ake samun musulmai na Alfahari da Ni’imar Musulunci har suna yin gori da ita.
Malam yace ana zagin Wadanda ba musulmai ba da sunan Arna masu fitsari a tsaye sai kuma ga wasu malamai sun bayyana suna cewa, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ma yana fitsari a tsayen.
Malam ya bayyana hakanne a wani Bidiyonsa da yake wa’azi wanda ya yadu sosai.