
Bayan wasan Supercopa de Espana da aka yi tsakanin Real Madrid da Barcelona wanda Barca ta yi nasarar cin kwallaye 3-2 ta dauki Kofin, Kylian Mbappe yayi wani da ya jawo cece-kuce.
Bayan da aka kammala baiwa Real Madrid sarkar girmamawa kuma ‘yan Barcelona suka tafa musu.
Mbappe ya hana ‘yan Madrid tsayawa su tafawa ‘yan Barcelona bayan da aka basu kofin.
An ganshi a wani Bidiyo yana ta kiran abokan wasansa da su bar gurin.
Lamarin ya raba kawunan mutane inda wasu suka ce hakan daidai ne amma wasu suka ce be kyauta ba.