Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon: Ban ce Ahlussunah basa son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba, cewa nayi ‘yan Dariqa sun fi Ahlussunah na yanzu son Annabi, kuma ina nan akan bakana>>Inji Sheikh Nura Khalid

Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid, Wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, bai ce ‘yan Izala basa son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba.

Abinda ya fada shine ‘yan Darika sun fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).

Yace dalilinsa kuwa shine su sufaye sun ce duk Hadisin da ya kawo aibu ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basa neman ingancinsa ko rashin ingancinsa, basu yadda dashi bane.

Hakanan duk Hadisin da ya kawo Yabo ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) suna yadda dashi ba tare da neman inganci ko rashin inganci ba.

Yace su kuma Ahlussunah na yanzu suna neman Hadisai da suka aibata Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ne suna karantar da mutane.

Karanta Wannan  Najeriya ta ware biliyan 60 na ciyar da ƴan firamare a 2025

Malam yace to a tsakaninsu waye yafi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *