
Matasa a jihar Kebbi sun fito gangami dan neman EFCC ta saki tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da take rike dashi.
An ga matasan dauke da kwalaye mau dauke da rubutun nuna goyon baya ga Abubakar Malami.
EFCC dai ta kama Abubakar Malami ne bisa zargin almundahanar kudade masu yawa ciki hadda na Abacha da aka kwato.