
Abokin Tauraruwar Tiktok, Babiana, Watau, G-Fresh Al-amin ya bayyana cewa wanenen ya tabo masa Babiana?
Ya bayyana hakane a martanin bidiyon da ta yi tana kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kawo mata dauki saboda a cewarta ‘yan Arewa musulmai sun sata a gaba suna cin zarafinta da zagi da barazana bayan fitar Bidiyo ta da aka ganta ba kaya a jikinta.
A cikin Bidiyon an ji ta tana cewa, shin irin abinda addininku ya koyar daku kenan?
Tace shin wane irin musulmai ne ake dasu yanzu inda tace bari dai ta yi shiru kar ta ce komai.
Watakila wadannan kalamai ne suka sa G-Fresh Al’amin ya gargadi cewa, idan Babiana ta fita daga Musulunci laifinkune.