
Rahotannin dake fitowa daga jihar Nasarawa na cewa, an sake yin garkuwa da dalibai da ba’a san adadinsu ba a makarantar Peter’s Foundation Secondary School dake Rukubi, a karamar hukumar Doma, Kamar yanda shafin @ChuksEricE suka ruwaito.
Rahoton yace ‘yan Bindigar sun shiga makarantar ne suka rika zabar daliban da zasu yi garkuwa dasu.
A Bidiyon da ya bayyana an ga iyaye sun shiga makarantar inda suka rika dauke ‘ya’yansu.
Tuni hukumomi suka bayar da umarnin Rufe makarantar, kamar yanda rahoton yace.
jaridar Sunnews ta tabbatar da rahoton sace daliban inda tace tana kokarin jin ta bakin hukumar ‘yansanda ta jihar.
jaridar tace wasu shaidu sun tabbatar mata da satar daliban.
Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan yin garkuwa da dalibai a jihar Naija, hakanan kwanaki kadan bayan yin garkuwa da dalibai a jihar Kebbi.