
Sanata Natasha Akpoti ta tashi a zauren majaliar Dattijai inda ta kawo shawarar a yi kira ga hukumomin Immigration na Najeriya da su hada kai dana kasar Libya dan dawo da matan Najeriya da ke tsare a gidajen yarin kasar Libya.
Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewa, irin wadanan mata an yi safararsu ne kuma ana musu fyadde suna haihuwar yara a gidajen yarin.
Dan hakane ta nemi a dawo da irin wadannan mata gida Najeriya.
Saidai wannan kiran nata bai samu karbuwa ba.
Inda sanatoci da yawa suka ki yadda su goyi bayanta.
Sai daga karshe ne aka samu Sanata daya ya goyi bayanta.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda aka rika sukar Sanatocin da nuna wariya ga Sanata Natasha a kuma nuna rashin kulawa ga ‘yan Najeriya.