
Baffa Hotoro yawa Dr. Hussain Kano wankin babban bargo kan kalaman da yayi na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba.
Baffa Hotoro yace wannan magana akwai wauta, Hauka, da Jahilci a cikinta.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyon martani da yawa Dr. Hussain Kano.
Yace ko Annabi Ibrahim AS sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi, duk da kasancewar Annabi Ibrahim AS badadin Allah ne
Yace dan haka kuskurene tunanin wai me laifi ne kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama ko kuma ace wanda suka cancanci shiga wutane kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama.
Yace dan haka suna baiwa Dr. Hussain Kano shawarar ya daina wa’azi, ya koma yayi karatu tukuna.