
Shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa doka ta hana kama ‘yan Bindiga da suka fito yin Sulhu.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai i da yake amsa tamyar me yasa ake ganin jami’an ‘yansanda tare da ‘yan Bindiga idan an zo yin sulhu
Yace idan dai suka fito suka nemi Sulhi, doka ta hana a kamasu.
Sannan ya yi kira ga jama’a da su daina cin zarafin ‘yansanda saboda sun saba musu
Yace idan dansanda ya saba maka, ka kai kararsa wajan ogansa.