
Attajirin Dan kasuwa, Aliko Dangote yace a lokacin da ya je zai gina matatar mansa, akwai gidajen Bokaye masu bautar gumaka guda 19 a wajan.
Yace kowa tsoronsu yake babu wanda ke iya zuwa wajan.
Yace Sarkin Yarbawa, Oni of Ife ne ya je wajan ya ce a rushe gidajen Bokayen.
Dangote yace ba dan haka ba da ba zasu samu damar gina kamfanin nasu ba.