
Ministan kudi, Wale Edun ya dawo gida Najeriya bayan jinyar da yayi a kasar Ingila.
Wale Edun ya dawo Najeriya ne tare da tawagarsa.
A baya dai an yada cewa Ministan ya kwanta rashin lafiya inda cutar shanyewar rabin jiki ta kamashi.
Saidai daga baya Gwamnati ta musanta cewa ba cutar shanyewar rabin jiki bace ta kamashi amma dai da gaske bashi da lafiya.