
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya tabbatar da kama sojojin da aka kai su bayar da tsaro a makarantar ‘yan Mata dake jihar Kebbi amma suka tafi shagalinsu aka je aka dauke ‘yanmatan.
Ministan yace an kama sojojin ana kan Bincike kuma idan aka tabbatar da abinda ake zarginsu za’a musu hukunci daidai da abinda doka ta tanada.