
Aƙalla mutane 151 ne suka samu raunuka bayan sun durgo daga dogayen gine-gine saboda tsoron da girgizar ƙasa ta haifar, a cewar ofishin gwamnan Istanbul.
Ofishin ya kuma wallafa a shafinsa na X, cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma babu wani gini da mutane ke zaune a ciki da ya ruguje.
Sai dai wani gini wanda babu kowa a ciki ya ruguje sakamakon girgizar ƙasar.
Ministan ilimi na Turkiyya, Yusuf Tekin ya sanar da cewa za a rufe makarantu na kwana biyu Alhamis da Juma’a.
Aƙalla an samu girgiza sau 51 a birnin a ranar Laraba, inda mafi girmansu ya kai ƙarfin maki 6.2, wanda ya shafi Istambul tun da fari, a cewar ministan cikin gida, Ali Yerlikaya.
Tuni masana kimiyya sun ce babbar girgizar ƙasa za ta iya afkawa birnin a kowane lokaci, hakan ya sa a abin da ke faruwa a yanzu ya sanya fargaba a cikin zukatan mazauna birnin.