
Attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa akwai ban haushi sosai yanda wasu mas kudi ke kashe Miliyoyin kudade wajan sayen motocin Alfarma da jiragen sama.
Yace wani lokacin idan yayi tafiya da jirginsa, babu ma wajan da zai ajiyeshi saboda duk filin jirgin an cikeshi da jiragen mutane.
Yace maimakon wannan barnar kudin, kamata yayi ace masu kudin sun bude kamfanoni ne ta yanda Dukiyarsu zata habaka kuma su samarwa matasa ayyukan yi.