
Rahotanni daga Madina na cewa, Tsohon shugaban jam’iyyar APC da tawagarsa sun isa birnin dan halartar jana’izar Marigayi Aminu Dantata.
A cikin tawagar Ganduje akwai sanata Barau Jibrin da sauransu.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan saukar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC.
Sauran wanda suka tafi Madina sun hada da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihawa, Umar Namadi, da sauransu.
Akwai kuma tawagar shugaban kasa wadda ministan tsaro, Abubakar Badaru ya jagoranta.
Tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shima ya tafi Madinan.