
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauka a garin Maiduguri a ziyarar da yake yi a jihar Borno.
Shugaban zai kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta Gudanar ne.
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum da tsohon Gwamnan Jihar, Madu Sheriff ne suka tarbi shugaban a filin jirgin sama na Muhammadu Buhari.