
Bidiyon wani babban sojan Najeriya na ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, shine ya dakile Yunkurin juyin mulkin da aka yi zargin an shiryawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
An ga sojan na ta rawa a wajan wani biki.
Da yawa dai sun rika jinjinawa sojan da cewa dan kishin kasane duk dai labarin a kafafen sda zumunta kawai yake ta yawo.
Sojoji sama da 40 ne dai rahotanni suka ce aka kama bisa zargin yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki.
Saidai Hukumomin gidan soja da Gwamnatin tarayya basu bayyana cewa yunkurin juyin mulkin ne akawa shugaban kasar ba.
Hakanan shugaban kasa Tinubu ya canjawa sojojin Najeriya da yawa wajan aiki.