Wasu mutane da suka kaiwa shehunsu ziyara sun rika rokonsa akan ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur da ake ciki.
An ji suna gayawa shehun cewa, tsadar man fetur din ta hana ziyara.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta inda wasu ke kafurtasu wasu kuma na karesu.