
Wani bincike da BBC ta yi ya gano yanda ake kai ‘yan mata daga Afrika Dubai suna karuwanci.
Binciken yace ba karuwanci kadai ake kai ‘yan matan yi ba, hadda ci musu zarafi ta hanyar yin futsari da kashi a jikinsu.
Hakan ya fara fitowa fili ne tun bayan da wata da aka kai ta yi irin wannan abu tace ba zata yi ba inda ta kwammace ta fado daga Bene ta mutu.
Daya daga cikin irin wadannan ‘yan matan da aka kai da aka yi hira da ita tace ko sun kira ‘yansanda basa daukar wani mataki akan lamarin.
BBC tace ta yi kokarin tuntubar ‘yansandan amma basu bata hadin kai ba.