
Rahotanni daga jihar Edo sun ce Karuwai ko mata masu zaman kansu ne da yawa aka kama aka gurfanar a gaban kotu saboda aikata aikin karuwanci.
A Bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga yanda matan masu zaman kansu ke rufe fuska yayin da suka yi layi suka shiga cikin kotun.
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke ganin cewa, ‘yan Bindiga ne ya kamata ace an kamo ana hukuntawa kamin karuwan.