
Dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda yace Turawa ke satar danyen man fetur daga Najeriya fiye da wanda Gwamnatin Najeriyar ke samu.
Yace ya je inda ake hako man fetur amma aka hanashi karasawa ainahin inda ake fitar da man.
Yace shugaban wajan ya kawo masa makudan kudade yace ya karba ya hakura da maganar zuwa ya gani dan kuwa idan yace sai ya je ya gani za’a iya kasheshi.
Yace baturen dake aiki a wajan ya gaya masa cewa ko turawa nawa za’a kashe sai an sake kawo wasu saboda irin man fetur din da suke samu ta barauniyar hanya ya kai kusan ganga Miliyan 5 a yayin da Gwamnati kuma ke samun ganga Miliyan 2.