Saturday, March 15
Shadow

Kalli Bidiyon yanda Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama bayan kwashe kusan shekaru 2 a Daura

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gidansa na birnin Kaduna daga Daura na jihar Katsina, a cewar tsohon mai taimaka masa na musamman Bashir Ahmad.

Buhari ya koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina tun bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023.

Tsohon shugaban ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna Uba Sani.

Akwai kuma sauran ‘yansiyasa da tsofaffin jami’an gwamnati da suka tarɓi shugaban a gidan nasa.

Kalli Bidiyon anan

Karanta Wannan  Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *