
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an samu fashewar tukunyar gas a wani wajan sayar da gas din dake Dorawar ‘yan Kifi, Rijiyar Zaki.
A bayanan da hutudole ya samu shine ba’a samu asarar rayuka ko jikkata ba saidai asarar Dukiya.
A bidiyon da suka rika yawo a kafafen sada zumunta, an ga da jin yanda tukwanen gas din duka rika fashewa kamar bam na tashi.
Saidai daga baya ‘yan kwana-kwana sun kai wajan sun kashe gobarar.