
Rahotanni daga garin Zaria, Jihar Kaduna na cewa, Harsasai sun fado daga cikin wata mota da ta je wucewa ta kofar jami’ar ABU dake garin.
Saidai kamin a ankara motar ta tsere.
An ga yanda mutane suka rika tattara harsasan dake zube a kan titi bayan tserewar motar.