‘
Yan majalisar Wakilai sun tattauna bukatar gayyatar gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Cordoso saboda zargin batan wasu kudade har Naira Tiriliyan 11.

Saidai kan ‘yan majalisar ya rabu inda wasu suka amince a gayyaci gwamnan CBN din wasu kuma sun ce basu amince ba.
Muhawara ta yi zafi akan hakan inda aka rika gayawa juna magana da nuna yatsa.