Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon yanda matar shugaban kasar Faransa ta fallamai mari a bainar jama’a

Ana zargin Matar shugaban kasar Faransa Brigitte Macron ta falla masa mari a yayin da suke shirin sauka daga jirgin saman da ya kaisu kasar Vietnam.

Suna cikin jirgin yayin da ana ganin shugaba Macron na magana da ita a yayin da ita kuma ba’a ganinta daga cikin jirgin sai aka ga hannunta ya falla masa mari.

Da farko ya gigice amma daga baya ya nutsu sannan ya fito daga cikin jirgin yayin da ta bishi a baya.

Yayi kokarin kama hannunta amma taki amincewa.

Karanta Wannan  Wannan abin kunya da yawa yake, A samu wasu su sasanta Sanata Natasha da Akpabio>>Inji Kungiyar Kiristoci ta CAN

Daga baya an ganshi cikin fushi.

Lamarin ya dauki hankula a kafafen sada zumunta.

Da farko ofishin Macron ya musanta Bidiyon da hotunan inda yace na bogi ne amma daga baya aka tabbatar na gaskiyane.

Saidai masu magana da yawun shugaban kasar sun ce wannan ba wani abin tayar da hankali bane, abu ne dake nuna irin shakuwar dake tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *