Friday, January 16
Shadow

Kalli Bidiyon yanda Matasa marasa jin magana suka tashi taron jam’iyyar ADC da aka yi a Kaduna wanda El-Rufai ya jagoranta, Matasan sun yi hakan ne a gaban ‘yansanda inda a cikin Bidiyon ake jin mutane na cewa menene Amfanin ‘yansandan?

A jiya ne dai rahotanni suka bayyana cewa, An kaiwa taron jam’iyyar ADC hari a Kaduna inda aka lalata dukiyoyi.

Taron wanda tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya jagoranta ya dauki hankula sosai.

Daga baya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya fito inda yake bayyana zargin Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da daukar nauyin wadanan ‘yan daban.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Duk wanda ya bayar da kudi wai a sauke masa Qur'ani dan kasuwancinsa ya bukasa yayi Bidi'a>>Inji Malam Jamilu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *