
Bidiyon yanda Ministan Ayyuka, Dave Umahi yayi yunkurin kamawa karamar Ministar harkokin kasashen waje, Bianca Ojukwu kugu ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Lamarin dai ya farune a yayin ziyarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Anambra.
Tuni dai ta ankare da abinda yake shirin yi inda ta yi caraf ta rike mai hannu.
Wasu dai na ganin dama can sun saba wannan dai kawai saboda a idon mutanene ake kokarin kare yawa.