
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Dan Gwagwarmaya, Omoyele Sowore da sauran masu zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu sun fito zanga-zangar.
Hakan ya kawo tsaikon ababen hawa sosai a Abujar.
Tuni dai jami’an tsaro suka budewa masu zanga-zangar wuta wanda hakan yasa suka tsere ciki hadda shugaban zanga-zangar, Sowore wanda aka ganshi yana gudu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore yace ‘yansandan sun kama Kanun Nnamdi Kanu da kuma Lauyansa sannan sun lakada musu duka.
Yace suna neman a sake su nan take.