Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon yanda shugaba Tinubu ya yiwa ‘yan matan Najeriya da suka lashe kofi Afrika murna, Ji abin mamakin da suka yi da ya dauki hankula sosai

Kungiyar ‘yan matan Najeriya dake buga kwallon kafa, Super Falcons sun lashe kofin gasar mata na nahiyar Africa bayan doke kasar Morocco da ci 3-2.

Wani bin mamaki shine, Har aka ke hutun Rabin lokaci, Morocco na cin Najeriya 2-0 wanda ana tunanin wasa ya kare.

Saidai bayan a aka dawo hutun rabin lokacine ‘yan Matan Najeriya suka nina azama suka rama kwallayen har suka kara kwallo daya a ragar Morocco wanda a haka aka tashi wasan 3-2.

Bayan nasarar tasu, Shugaba Tinubu ya kirasu a waya inda ya bayyana farin cikinsa da shaida mus cewa, Najeriya na Alfahari dasu.

Karanta Wannan  Taron rudaddu ne suka kafa jam'iyyar ADC>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *