
An gano cewa, Kuskuren hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar.
Akalla Dalibai Miliyan 1.5 ne suka ci kasa da makin da ake bukata a jarabawar ta bana wadda ake ganin sun yi yawa.
A yayin taron manema labarai dan bayyana dalilin da yasa aka samu wannan tangarda, shugaban hukumar ta JAMB, Professor Ishaq Oloyede ya fashe da kuka.
Ya dai bayar da hakuri sannan kuma ya sha Alwashin sakewa dalibai da yawa jarabawar.
Yankin da aka samu wannan matsaloli na jihar Legas ne da kudu maso kudu.