
Wata sabuwar dirama tsakanin Kakakin Majalisar Dattijai Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti ta faru a zaman majalisar.
Ana karanta wata sabuwar doka ce akan zubar da ciki amma akan jinginar da dokar dan sake dubata.
Bayan Godswill Akpabio ya sanar da dakatar da tattauna kudirin dokar, Sanata Natasha ta nemi a bata damar yin magana akan kudirin.
Saidai sauran sanatoci sun ce bata damar maganar bayan dakatar da tattauna kudirin ya sabawa dokar majalisar.