
‘Yan daba sun kai hari a unguwar Rigasa dake jihar Kaduna ranar Juma’a, 21 ga watan Ramadana wanda yayi daidai da ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2025.
Kakakin ‘yansandan jihar,DSP Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wani mazaunin unguwar Rigasan ne ya kirasu ya sanar dasu cewa, ‘yan daba daga Malalin Gabas, da Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko sun shiga unguwar dan farwa masallata.
Yace sun kai harinne Layin Bilya inda matashi dan sa kai da abokan aikinsa suka yi kokarin hanasu wucewa.
Saidai sun tarwatsa ‘yan sa kan inda suka bi matashin har cikin masallaci gaban liman suka kasheshi ta hanyar caccaka masa wuka.
kakakin ‘yansandan ya kara da cewa sun kama mutane 12 da ake zargi da hannu a lamarin.
Matashin da suka kashe, Usman Mohammad dan kimanin shekaru 23 tuni aka yi jana’izarsa kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.
Sannan yace an baza jami’an tsaro a yankin musamman kusa da masallacin da lamarin ya faru.