
Wani karamin sojan Najeriya ya bace bayan da ya bayyana cewa sojojin da aka jiwa rauni da kudaden Aljihunsu suke kula da kawunansu ba hukumar sojin ce ke kula dasu ba.
Sojan ya bayyana hakanne a wani bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Yace maganar gaskiya ya ji dadi da aka hana shugaban sojoji Visa zuwa kasar Canada, yace da ba’a hanashi Visar ba da ba za’a san cewa turawanne ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci ba.
Yace yana fatan a ci gaba da hana shuwagabannin sojojin Visa dan Asiri ya tonu ‘yan Najeriya su san halin da ake ciki game da matsalar tsaro.