
Likitoci a asibitin Devnandani Hospital, Hapur, dake kasar India sun ciro abubuwa 50 da wani mutum dan shekaru 40 ya hadiya daga cikinsa.
Likitocin sun kwashe awanni 5 suna wannan aiki, kamar yanda rahotanni suka bayyana.
Ranar 17 ga watan Satumba aka kaishi asibiti yana aman jini inda aka mai Scanning aka ga Cokulan karfe 29 da burosh 19 da kuma biro guda 2.
Lamarin ya baiwa likitocin mamaki.

Shugaban Likitocin da suka yi wannan aiki, Dr. Shyam Kumar ya bayyana cewa, bai taba ganin irin wannan abubuwan a cikin mutum daya ba.
Ya kara da cewa an babballa abubuwan kamin mutumin ya hadiyesu.
Mutumin ya aikata hakanne bayan da aka kaishi wani gidan horo da baya so.
Rahoton yace yana samun sauki bayan da aka masa aiki.