Tuesday, May 13
Shadow

Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya aika wakili zuwa wajan daurin auren Rarara

Mallam Abdulaziz Abdulaziz Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Tinubu Wajen Halartar Ɗaurin Auren Rarara Da A’isha Humaira.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya wakilta mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Mallam Abdulaziz Abdulaziz wajen halartar ɗaurin auren shahararren mawaƙin jam’iyyar APC, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) da amaryarsa, A’isha Humaira.

Auren wanda aka ɗaura yau a garin Maidugurin Jihar Borno, ya samu halartar mataimakin shugaban majalissar dattawa ta ƙasa, Sanata Barau Jibrin, da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari sauran manyan mutane da dama, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

“Duba da alaƙar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Dauda Kahutu Rarara, Shugaban ƙasa Tinubu ya ce lallai a zo wannan ɗaurin aure a wakilce shi domin a yi musu fatan alkhairi a kuma nuna cewa ana tare wannan abu namu ne na gida. Muna yi musu fatan alheri, Allah Ya ba su zaman lafiya da zuri’a ta gari”. Cewar wakilin shugaban ƙasa, Mallam Abdulaziz Abdulaziz.

Karanta Wannan  Dattijo Edwin Clark ya rasu yana da shekara 97

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *