
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi, NDLEA sun fuskanci matsalar harin kwantan Bauna da aka kai musu yayin da suka kai samame kan wasu masu harkar miyagun kwayoyi a Jahi dake Abuja.
Jami’an NDLEA sun kai samamenne bayan da suka samu bayanan sirri game da harin inda suka shiga wani kango suka kwace kwayoyin.

Saidai a yayin da suke shirin ficewa daga cikin kangon, maharan sun bude musu wuta inda aka jikkata ma’aikatan hukumar su 3.
Daya daga cikin ma’aikatan an sameshi ne a kirjinshi inda daya kuma sauran aka samesu a kafa.
Tuni dai aka garzaya dasu Asibiti dan basu kulawa ta musamman.
Shugaban hukumar, Brig Gen Mohamed Buba Marwa (Rtd) ya jinjinawa ma’aikatan asibitin Abuja bisa kulawar da suka baiwa ma’aikatansa inda kuma yayi magana da wadanda aka jikkara din tare da basu tabbacin hukumar zata yi dukkan mai yiyuwa waja ganin sun samu sauki da kuma hada kai da sauran jami’an tsaro dan gano wadanda suka aikata wannan laifi.