Saturday, March 15
Shadow

Kalli Hotuna:An tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano

‘Yan Bijilante sun tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala Tagarji dake Kano.

‘yan Bijilanten sun fita aiki ne da dare inda suka ga kwali a cikin wani rami an ajiye, nan suka budeshi suka ga ashe gawar jariri ne a ciki.

Kwamandan Bijilante din, Sulaiman Rabiu ne ya tabbatar da haka inda yace sun tsinci gawar jaririnne da misalin karfe 2 na daren ranar Asabar.

Yace sun dauki gawar zuwa ofishinsu inda suka kira me unguwa ya gani kamin daga baya su kai jaririn zuwa ofishin ‘yansanda.

‘Yansandan sun gaya musu cewa su tafi da gawar zuwa Asibiti dan a dubata inda likitoci suka tabbatar jaririn ya mutu.

Karanta Wannan  Bayan Amarya Ta Gudu A Safiyar Ranar Daurin Aurensu, A Karshe Ango Ya Auri Daya Daga Cikin Kawayen Amarya A Ranar Auren

Sulaiman yace sun yiwa jaririn sallah inda aka binneshi kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Daga baya dai ya jawo hankalin iyaye da su rika saka ido akan ‘ya’yansu, musamman ‘yan mata dan gujewa samun cikin shege.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *