
A wani Bidiyo da ya kara bayyana, an ga yanda tsageran daji suka yiwa sojojin Najeriya kwantan Bauna suka jikkata da yawa daga cikin sojojin.
An ji wani soja yana cewa, Albashin nawa akw biyanshi duka duka inda yace ba zai iya ba.
Jaridun Leadership da na Sahara Reporters duk sun tabbatar da wannan harin kwantan bauna da ‘yan Bindiga suka kaiwa tawagar sojojin da suka tafi kubutar da ‘yan mata ‘yan makarantar jihar Kebbin.

Babu dai wata sanarwa a hukumance da aka fitar.