
Hukumomin ‘yansanda sun kama Sojan Najeriya da ake zargi da satar mota.
Sojan ya hada kai da wani farar hula ne dan satar mota kirar Toyota Hilux a garin Legas.
An kama su biyunne a yayin da suke kokarin kai motar da suka sata zuwa kudancin Najeriya.
Sojan dake aiki a rundunar Operation Delta Safe dake jihar Bayelsa, ya bi dayan farar hular ne dan ya rika nuna ID card dinsa na aikin sojane ana barinsu suna wuce shingen jami’an tsaro.
Saidai ‘yansanda sun bi sahunsu suka kamasu a yayin da suke kokarin kai motar inda zasu sayar